Kasuwar Kirifto na Saƙale da Abubuwan da ke Faruwa a Amurka
Tattalin arziƙin ƙasar Amurka abu ne hamshaƙi, sannan da kuɗinsu ake kusan mafi yawan hada-hadar kasuwanci a kasuwar Kirifto.
Bugu-da-ƙari sun riga kowa karɓa da yarda da fasahar blockchain da yin amanna da kuɗin Kirifto na farko, wato Bitcoin.
Magana ta gaskiya Amurkawa suna daga cikin mafi tsoka a masu zunuzurutun liquidity a kasuwar kirifto.
Wannan ya sa kusan su ke juya kaso mafi girma na sashen kasuwar, duk ina baƙin labari ya fito daga ƙasarsu sai ku ga nan da nan kasiwa ta yi dim.
Ga masu son cin gajiyar kasuwar hada-hadar kuɗaɗen Kirifto, ina mai basu shawara da su rinƙa bibiyar abubuwan da ke wakana a Amurka domin cin gajiyar shiga trend tun yana ƙarami.
Sannan, mutum in a DEX ya ke trading, ya rinka ɗaukar tweets ɗin fitattu irin su Elon Musk, CZ Binance da sauransu a matsayin damar samun kuɗi.
Kirifto (Formerly Ahamat Desk)
April 3, 2025
If you are interested in more contents or airdrops like this then don't forget to follow us on Telegram, X(Twitter), Facebook, and Subscribe to our YouTube Channel that is where the real treasure is!